By Muhammad Ibrahim, Sokoto
Babban Limamin Masallacin Jumua na Professor Gwandu, Sheikh Yahuza Abubakar ya kalubalanci al’ummar Musulmi dasu kyautata ibadarsu a karshen wannan watan na Ramadan.
Yayi wannan kiranne yayin da Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto tare da Maigirma Ministan Kasa A Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtar Muhalli Barista Bello Muhammad Goronyo da sauran Shugabanni suka halarci Sallar Jumu’a a Masallacin Jumu’a dake unguwar Arkilla na Professor Abubakar Gwandu.
Bashar Abubakar ya kara da cewa Mallam Yahuza Abubaakar shi ne ya jagoranci hudubar da kuma bada sallar Jumu’ar.
Hudubar ta maida hankali ne ga falalar kwanakkin karshe na watan Ramadan wato goman karshe.
Ya bada shawarar maida hankali ga yin ibada Iya zarafi domin samun rahmar Allah madaukakin sarki.
Ya Kuma bukaci a kirdadi Daren Lailatul Qadr daga 21,23,27 da Kuma 29, Inda kacokan ya nuna muhimmancin tsayuwa ga kwanakin goma domin Kara kusanta ga ubangiji.
Sauran Jama’a da suka raka Maigirma Sanata a Masallacin sun haka da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Sokoto, Alh. Sulaiman Sarkin Fulani Ahmadu, Kwamishinan Ilimi mai zurfi Alh. Aminu Dodo Iyan Sokoto.