Gwamna Ahmed Aliyu yayi taaziyyar rasuwar Sheilkh Mode Abubakar

By Muhammad Ibrahim, Sokoto

Gwaman jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana kaduwa akan rasuwar daya daga cikin mashahurran malaman addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Mode Abubakar.

Gwaman ya bayyana rasuwar da cewa wani irin babban rashi ne ba wai ga iyalan marigayin ba, a’a har ma ga jiha da kasa baki daya.

Yace marigayin ya gudanar da ruyuwar sa ne a wajen karantar da mutane akida da kuma aikin Daawah don yada addinin Islama.

Gwamna Aliyu ya ce za’a ci gaba da tuna Ayukkan alkhairi da gwagwarmayar marigayin yayi na yada addinin musulunci a lungu da sako na jihar nan.

Mai ba Gwamna shawara kan harkokin yada labarai Abubakar Bawa ya kara da cewa,Alhaji Ahmed Aliyu ya roki Allah da ya karbi kyawawan ayukkan marigayin ya kuma shafe kura kuran sa.

Haka ma ya bukaci iyalan marigayin dasu dauki wannan rashi a matsayin wani abu daga Allah, yana mai rokon Allah da ya basu hakuri.

Kafin rasuwar sa dai Sheikh Mode Abubakar shine Babban limamin Masallacin Jumu’a na Makarantar Koyarda ilimin Alqurani da sauran ilmomuka ta sarkin musulmi Muhammadu Maccido.

See also  Sen Wamakko distributes relief mateirals to 500 orphans in Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *