By Muhammad Ibrahim,Sokoto
Mataimakin gwamnan jihar Sokoto Alhaji Idris Muhammad Gobir ya umurci karamar hukumar mulkin Sabon Birni da ta cigaba da daukar nauyin kula da magunguna ga wasu mutane 2 ‘yan uwan juna da ‘yan bindiga suka yiwa mugun rauni a kauyen Kyalkale dake cikin mazabar Tarah acikin karamar hukumar.
Alhaji idris Gobir yace mutanen biyu sun chanchanci samun taimakon magani saboda irin yanayin da suke ciki.
Haka kuma ya bada tasa gudummuwa ga mutanen biyun.
Da yake bayanin yadda lamarin ya kasance,mahaifin mutanen Malam Ilyasu Ibrahim yace kusan watanni 5 da suka shude,’yan bindigar sun kawo farmaki akansu a lokacin da suke gona suna aiki.
Yace ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikin ‘ya’yan nasa mai suna Adamu Ilyasu mai shekaru 8 ta hanyar yi masa yankan rago,yayin da suka yiwa yarsa mai suna Suwaiba Ilyasu mai shekaru 12 mugun yanka ga makoshi.

Yace saboda irin mugun yankan da suka yi mata,a yanzu ko magana bata iya yi.
Haka kuma,’yan bindigar sun sari kanensa mai suna Zubairu Isma’ila mai shekaru 25 sara ga kai da hannuwa da kuma kafa.
Yace irin mugun yankan da aka yiwa Suwaiba ga makoshi,ya sanya a yanzu bata iya magana dud da aikin tiyata na farko da akayi mata.
Malam ilyasu ya kara da cewa za’a gudanar da aikin tiyata na biyu nan gaba.
Shima da yake nasa tsokaci,kantoman karamar hukumar mulkin Sabon Birni Alhaji Garba Kaba ya yi alkawalin cigaba da taimakawa wajen samar masu magani
Yace tun lokacin da hatsarin ya faru,karamar hukumar ta taimaka wajen samadda maganin ga wadanda aka raunata.