Gwmnan Jihar Sokoto ya bayarda Kyautar N30,000 ga ilahirin maaikatan jiha

By Muhammad Ibrahim, Sokoto

Mai Sakataren hulda da ‘Yan jarida a offishin Gwamna, Abubakar Bawa yace mai girma gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, ya aminta da bayarda kyautar Goron Sallah ga ilahirin ma’aikatan jiha dana kananan hukumomi da masu fansho da kuma masu karbar alawus alawus a kananan hukumomi da kuma hukumar kula da lafiya a matakin farko a fadin jihar nan.

Wannan biyan goron Sallah dai za’a yi shi a rukuni biyu.

Rukuni na farko ya hada da ma’aikatan Jiha, dana kananan hukumomi wadanda zasu karbi naira dubu talatin N 30,000 kowanensu a matsayin goron Sallah.

Sai kuma rukuni na biyu wadanda ya hada masu karbar fansho da masu karbar alawus alawus a kananan hukumomi da kuma masu karbar alawus alawus a hukumar kula da kiyon lafiya a matakin farko wadanda zasu karbi naira dubu Ashirin kowanensu N20, 000 a matsayin goron Sallah.

Shi wannan biyan goron Sallah dai da za’a soma shi a gobe Alhamis 13 ga watan nan da muke ciki dai nada manufar ganin ma’aikatan sun gudunar da bukukuwan Sallah cikin sauki.

Haka ma gwamnan ya aminta da biyan kudaden tafiyar da Ofisoshin gwamnati wato CA na wannan watan da muke ciki.

Idan dai za’a iya tunawa kwanaki 3 da suka shude gwamnan ya bada umarnin biyan albashin watan yunin nan da muke ciki ga ilahirin ma’aikatan jiha da zummar ganin an saukakawa ma’aikata don su gudanar da shagulgulan sallah babba cikin tsanaki.

Gwamna Ahmed Aliyu Wanda a yanzu haka yake can kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajj, ya bukaci ma’aikata da su sakawa wannan kokari da gwamnatin sa ke Yi musu ta hanyar kiyayewa da zuwa aiki cikin lokaci.

See also  UBEC, SUBEB conduct 5-day ECCD training in Sokoto

Haka ma yayi addu’ar samun nasara gudanarda shagulgulan sallah lami lafiya a jihar nan da kasa da kuma duniya baki daya.

Idan dai zaa iya tunawa tuni da ma’aikatan jihar nan suka soma samu alert na albashin wannan watan kamar yadda gwamnan ya bada umarni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *