By Muhammad Ibrahim, Sokoto
A wani bangare na shirye-shiryen bukin yaye Dalibai na bana wanda Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto zata gudanar yau Assabar, zata karrama daya daga cikin fiitattun Malaman dake akwai a jihar Sokoto, Goni Mallam Bello Boyi da Digirin Karramawa na Dokta.
A haka ne, Goni Mallam Bello ya kawo ziyara a wajen Mamba a Majalisar Koli ta Hadin Kan Kasashen Musulmi ta Duniya mai Mazauni a Birnin Makka, Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto domin gabatar masa da takardar shaida ta wannan karramawar.
Mai magana da yawun Sanata,Bashar Abubakar yace Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya nuna jindadin sa da kuma yiwa Goni fatan alheri Kan wannan matsayin da Jami’ar ta shirya bashi.